An raba buhunan shinkafa 3,071 da masara 3,071 da taliya 2,000 ga mabukata a karamar hukumar Malam Madori
Kwamshinan harkokin Masarautu da Kananan hakumomi na jihar Jigawa Ahmad Garba MK ya nuna gamsuwar sa yadda rabon kayayyakin tallafin abincin azumin Ramadana daya gudana a karamar hakumar Malam Madori.
Kayayyakin da aka raba sun hada buhunan shinkafa dubu 3,071 masu nauyin kilogiram 10, da buhunan masara 3,071 da katan din taliya dubu 2 ga talakawa da mabukata a fadin mazabun 11 dake karamar hakumar.
A nasa jawabin shugaban karamar hakumar Malam Madori Alhaji Hussaini Umar BK ya godewa gwamnatin jiha, yana mai tabbatar da rabon kayayyakin ga wadanda suka dace. Kayayyakin dai sun kasance daga cikin wadanda gwamnatin jiihar jigawa ta ware, da suka hada buhunan shinkafa dubu 150, da na masara dubu 150, da kuma katan din taliya dubu 100.