Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta biyan diya ga iyalan sojoji 17 da aka kashe

0 110

An gabatar da bukatar ne a zaman majalisar na jiya Talata, yayin da Sanatocin suka yi shiru na minti daya domin karrama sojojin da suka rasa rayukansu a ranar Alhamis a yankin Okuama da ke jihar Delta.

A yayin zaman, shugaban kwamitin majalisar dattawa a bangaren sojojin, Sanata Abdulaziz Yar’adua, shine ya gabatar da kudirin na gaggawa kan kashe jami’an sojin da kuma wajabcin gudanar da bincike cikin gaggawa.

Daga nan kuma aka ba da umarni ga kwamitocin sojoji da sojojin ruwa da na tsaro da su hada kai da rundunar sojin domin gudanar da bincike kan lamarin. An kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tabbatar an gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aikar, tare da kama su, a hukunta su, ta hanyar da  doka ta tanada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: