Dakarun sojin Najeriya sun kai sumame wata maboyar masu ayukkan yan tada kayar baya

0 131

Dakarun sojin Najeriya sun kai samame a wata maboya a Palele da ke kusa da Shiroro a jihar Neja inda ayukkan yan tada kayar baya yayi kamari.

Sojojin, yayin da suke aikin sintiri na sirri sun hango wasu tarin makaman ‘yan ta’adda a Gabashin Palele, inda nan take suka wargaza maboyar tare da lalata makaman.

Kakakin rundunar sojin saman, Edward Gabkwet, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai, ya ce an samu nasarar lalata maboyar, ciki har da lalata makamai da alburusai.

Gabkwet, ya bayyana cewa ana kyautata zaton makaman na da alaka da wani shugaban ‘yan ta’adda wanda ke cikin jerin sunayen ‘yan ta’adda da ake nema ruwa a jallo.

Leave a Reply

%d bloggers like this: