Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudurin dokar bada hutun zaman makoki

0 138

Majalisar wakilai ta yi karatu na biyu ga kudurin dokar da zata bayar da izinin baiwa ma’aurata hutun  zaman makoki bayan rasuwar abokan zaman su.

Kudirin ya bayar da shawarar cewa, bazawara za’a bata hutun takaba na wata biyar, yayin da namijin da matar sa ta mutu za’a bashi hutu na wata daya tare da cikakken albashi.

A muhawarar da ya jagoranta a zauren majalisar a jiya Talata, dan majalisar wakilai Abdullahi ya ce mutuwa ta na yin illa ga ma’aurata idan suka rasa abokan zamansu, don haka suna bukatar lokaci don yin jimami cikin wani kayyadadden lokaci. Dan majalisar ya yi nuni da cewa, a mafi yawan al’adu da addinai a Nijeriya, akwai tanadin zaman makoki ga mata, don haka akwai bukatar a hukumance a samar da lokacin da doka ta amince da ita ga ma’aurata su yi jimamin mutuwar abokan zamansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: