Donald Trump ya buƙaci sakin mutanen da suka afka majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu

0 80

Dan takarar shugaban Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump, ya buƙaci sakin mutanen da suka mamayi majalisar dokokin ƙasar a ranar 6 ga watan Janairu. Mista trump na magana ne bayan hukuncin da kotun koli ta yanke, da ke cewa masu gabatar da ƙara sun zaƙe, wajen amfani da dokar hana tayar da zaune tsaye yayin gurfanar da mutanen a gaban kotu. Tsohon shugaban ƙasar na Amurka ya kuma jefa ayar tambaya kan goyon bayan da ƙasar ke bai wa Ukraine, bayan ya yi iƙirarin nasara a muhawarar da suka fafata da shugaba Biden na jam’iyyar Democrat. Donald Trump ya ce shi ya zama gwarzon muhawarar ”duk da cewa abokin muhawarata ya samu duka abubuwan da yake so kafin fara muhawarar, kamar ranar da yake so, a kafar da yake so, da alƙalan da yake so, amma duk da haka ya kasa kare kansa”.

Leave a Reply

%d bloggers like this: