An kama mutane 1,137 a jihar Kaduna da ake zargi da aikata laifuka daban-daban

0 128

Jami’an ‘yan sandan jihar Kaduna sun kama mutane 1,137 da ake zargi da aikata laifuka a cikin watanni biyun da suka gabata. Da yake jawabi ga manema labarai jiya a hedikwatar rundunar da ke Kaduna, kwamishinan ‘yan sandan (CP), Audu Dabigi, ya ce wadanda ake zargin sun hada da ‘yan fashi da makami 73, masu garkuwa da mutane 79 da kuma masu satar waya 985. Da yake bayar da cikakken bayani game da kama mutanen, ya ce an samu wani da ake zargi da laifin barna a hanyar jirgin kasa – mai suna Naim Mikaila, mazaunin Kajuru, dauke da karafunan titin jirgin kasa guda 100 ba tare da bayar da gamsasshen bayani ba.Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yan sanda (IG) Kayode Egbetokun, bisa jajircewarsa wajen shugabanci. Dabigi ya kuma yabawa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani kan goyon bayansa da kuma jajircewarsa na inganta harkokin tsaro a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: