Wata babbar mota ta buge akalla 14 da hakan yayi sanadiyyar rasa rayu kansu a jihar Kano

0 217

A jiya Juma’a ne wata babbar mota da ke tafiya a cikin garin lmawa da ke karamar hukumar Kura ta jihar Kano ta buge akalla 14 da hakan yayi sanadiyyar rasa rayu kansu. An samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a lokacin da motar ta yi karo da masallatan da suke dawowa daga masallacin Juma’a bayan kammala sallar Juma’a.Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa reshen Kano, CC Ibrahim Abdullahi wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, ya ce mutane da dama sun samu raunuka daban-daban. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, CRC Abdullahi Labaran, ya ce rahotannin farko sun nuna cewa motar ta rasa yadda za ta yi, inda ta yi karo da masu tafiya a kafa da suka kammala sallar Juma’a.Kwamandan sashin ya ce ana ci gaba da kokarin gano hakikanin abin da ya janyo afku hatsarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: