Gwamnatin Jigawa za ta tattauna kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata a jihar

0 249

Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya ce gwamnatinsa za ta tattauna kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata a jihar.Kungiyoyin kwadago sun shiga tattaunawa da gwamnatin tarayya kan sabon mafi karancin albashin. Duk da cewa an bayar da Naira Dubu 62,000, amma wasu kungiyoyin kwadago sun ki amincewa, Gwamnan Jigawa ya ce duk abin da Gwamnatin Tarayya ta dauka a matsayin sabon mafi karancin albashi, gwamnatinsa za ta tattauna da ma’aikatan jihar kan abin da za ta biya. Gwamna Namadi ya ce sun kafa kwamitin bangarori uku da suka hada da ma’aikata da masu ruwa da tsaki  kan sabon mafi karancin albashin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: