ECOWAS da AU sun tura tawagar hadin guiwa ta binciken gaskiya kafin zaben kasar Laberiya

0 206

Gabanin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokokin kasar Laberiya da aka shirya gudanarwa a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2023, kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da kungiyar Tarayyar Afirka (AU) sun tura tawagar hadin guiwa ta binciken gaskiya kafin zaben kasar domin tantance halin da kasar ke ciki na shirin gudanar da zabe.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kungiyar ECOWAS ta fitar a daren jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce, tafiyar ta ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli na karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe ta kasa, da Ambasada Calixte Mbari, shugaban dimokradiyya.

Sauran mambobin tawagar sun hada da Ambasada Haja Alari Cole, mamba a majalisar ta ECOWAS da  Ms Jean Mensa, shugabar hukumar zaben kasar Ghana; da Mista Elyse Ouedraogo, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasar Burkina Faso. Sauran sun hada da Muhammad Sulaiman Isa, mataimakin jakadan Najeriya a kungiyar ECOWAS; Dr Cyriaque Agneketom, Daraktan wanzar da zaman lafiya da tsaro na ECOWAS; da kuma wata tawagar kwararru ta hadin gwiwa daga Hukumar ECOWAS da AU.

Leave a Reply

%d bloggers like this: