Kimanin mutane miliyan 11 ne ke mutuwa a duniya sakamakon karancin abinci mai gina jiki

0 222

Kwararru a fannin abinci mai gina jiki sun yi kira da a samar da ingantattun tsare-tsare don magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a kasar, inda suka kara da cewa kimanin mutane miliyan 11 ne ke mutuwa a duniya sakamakon karancin abinci mai gina jiki.

Sun yi wannan kiran ne a wani taron bita da aka shirya a jiya wanda kungiyar Tattalin Arzikin Kasa (NESG) tare da hadin gwiwar Cibiyar Bayar da Shawara ta Civil Society Legislative Advocacy Centre (CISLAC) da eHealth Africa, wanda ke dauke da taken, ‘Tabbatar da Yarjejeniyar Abinci ta Ma’aikata don Inganta Lafiya da Jin Dadi a Ma’aikatan Najeriya.

Wata kwararriya a tsarin abinci mai gina jiki, Mrs Dolapo Enejoh, ta jaddada bukatar samar da tsayuwar manufa don magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a kasar,

Shima da yake jawabi, shugaban kwalejin kimiyyar abinci da ilimin dan Adam na jami’ar tarayya ta aikin gona Abeokuta (FUNAAB) kuma shugaban kungiyar abinci mai gina jiki ta kasa, Farfesa Wasiu Afolabi, ya ce bangaren gwamnati ba shi da tsarin samar da abinci na ma’aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: