An fara gudanar da bincike a kan yadda ake sayar da barasa ‘mafi guba’ a Ogun

0 253

A jiya ne gwamnatin jihar Ogun ta ce ta fara gudanar da bincike a kan yadda ake sayar da barasa ‘mafi guba’ a wasu sassan jihar.

Gwamnatin ta ce hakan ya biyo bayan mutuwar wasu mazauna jihar bayan da aka ce sun sha barasa a makon jiya.

Gwamnati ta ce ta samu rahotannin mutane 11 da suka kamu da munanan cututtuka da kuma mutuwar mutane takwas wadanda ke da alaka kai tsaye da shan kayan maye a cikin gida.

Mai ba gwamnan jihar shawara na musamman kan harkokin kiwon lafiya, Dakta Tomi Coker, a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya a Abeokuta, ya gargadi al’ummar jihar game da shan barasa da aka hada a gida da sauran kayayyakin da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta amince da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: