Faransa za ta rufe ofishin jakadancinta a Nijar

0 235

Faransa za ta rufe ofishin jakadancinta a Nijar, inda ake nuna kyama ga Faransawa tun bayan juyin mulkin da aka yi a watan Yuli.

Hakan ya sanya  ficewar  ma’aikata bayan kai wani hari lamarin da ya kawo cikas wajen gudanar da aiki a ofishin.

Dangantaka tsakanin Nijar da kasar Faransa ta yi tsami bayan da sojoji suka hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum a juyin mulki a ranar 26 ga watan Yuli. Dakarun Faransa da ke da hedkwata a Nijar a wani bangare na yaki da masu ikirarin Jihadi zai kammala janyewarsu a wannan watan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: