Rundunar ‘yan sanda ta dakatar da wasu jami’anta bisa kama su da laifin tursasawa wajen karbar cin hanci

0 177

Rundunar ‘yan sandan jihar Oyo, ta dakatar da wasu jami’anta biyu Jimoh Lukman da Kareem Fatai sakamakon kama su da laifin tursasawa wajen karbar cin hanci.

Tuni aka tube musu kakin ‘yan sandan bayan hukumar ta same su da aikata wannan laifi.

Sawaba rediyo ta gano cewa jami’an ‘yan sandan biyu an kore su daga aikin ne biyo bayan wani faifan bidiyo da ya nuna yadda suke kokarin tursasa wani dan kasar Netherland ya basu cin hanci lokacin da yake kan babu kirar Bike akan hanyar Abuja.

Kwamishinan ‘yan sanan jihar Adebola Hamzat, yayin da yake tube musu kakin ‘yan sandan a Ibadan, yace dakatarwa ya biyo bayan rahoton bincike da aka gudanar. An dauki bidiyon yadda jami’an ke kokarin tursasawa dan kasar Netherland ya ba su cin hancin ranar  29 ga watan Nuwamba 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: