Fulata ya gabatar da bukatar biyan malaman firamare albashin ₦250,000 a Najeriya

0 204

Shugaban kwamitin majalisar wakilai mai kula da ilimin jami’o’i, Dr. Abubakar Hassan Fulata ya gabatar da bukatar biyan malaman firamare albashi dubu dari biyu da hamsin a kasar nan.

Ya kuma shigar da bukatar  Naira miliyan daya a matsayin albashin malaman jami’oi.

Dan majalisar ya ce matakin zai inganta harkar koyo da koyarwa a najeriya

Ya ce gwamnatin tarayya ta cire Jami’o’i daga tsarin biyan lbashi na bai daya wato IPPIS.

A cewarsa gwamnatin tarayya za ta ware kudi a cikin kasafin kudin shekarar 2025 domin kaddamar da sabuwar kwalejin noma ta tarayyaa  Kiri-Kasamma da Kwalejin Ilimi ta tarayya a Birniwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: