Fursunoni fiye da 100 a gidajen kaso na Jihar Kano na neman a yi musu afuwa

0 189

Fiye da fursunoni 100 ciki har da waɗanda ke cin sarka kan laifin kisan kai a gidajen kaso na Jihar Kano na neman a yi musu afuwa.

Kwanturolan Gidan Yarin Kano, Mista Suleiman Inuwa ne ya bayyana hakan da cewa fursunonin sun miƙa buƙatar neman a yi musu aikin gafara.

Mista Inuwa ya bayyana hakan ne yayin da kwamitin yi wa fursunoni afuwa karkashin jagorancin Hajiya Azumi Namadi Bebeji ya ziyarci Gidan Yarin da ke Janguza.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Gidajen Yarin Kano, Musbahu Kofar Nassarawa ya fitar jiya juma’a. Sanarwar ta ce daga cikin fursunonin da ke neman afuwar har da waɗanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai da ke fama da ƙalubale na rashin lafiya da kuma dattawa waɗanda suka manyanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: