Gwamnan jihar Bauchi ya amince da bada tallafawa maniyyatan jihar da kashi 50 cikin dari

0 201

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya amince da bada tallafin kashi 50 cikin dari ga maniyyatan jihar, biyo bayan karin kudin kujerar aikin hajjin bana da aka yi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, gwamnan ya ce duba da halin matsin tattalin arzikin da kasar nan ke ciki, ya amince da biyan rabin kudin aikin hajjin da aka karawa maniyyata.

A makon da ya gabata ne Sawaba radio ta ruwaito cewa, Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta kara kudin kujerar aikin hajjin bana ga maniyyata zuwa kasar Saudiyya da naira miliyan daya da dubu 918 da 32 kobo 91.

Gwamnatin tarayya a wani bangare na kokarin inganta tattalin arziki, gwamnatin ta fitar da kudi naira biliyan 90 domin tallafawa maniyyata aikin hajjin bana a kasa mai tsarki. Haka kuma wasu jihohi kamar Kano, Kebbi, Bauchi Kogi, da Ogun sun bayar da tallafi ga maniyyatan aikin hajjin bana da suka fito daga jihohinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: