Ganduje ya bukaci gwamnonin kasar nan da mataimakan su da su rike kyakywar alakar dake tsakanin su

0 255

Shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnonin kasar nan da mataimakan su da su rike kyakywar alakar dake tsakanin su domin cigaban dimokaradiyya a Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Kanon, ya fadi haka ne yayinda ya karbi bakuncin wasu tsoffin mataimakan gwamnaoni na jam’iyyar APC jiya a Abuja.

Ganduje yace,kasancewa mataimakin gwamnan abun ne ma matukar wahala, saboda ana samun wadanda ke rura wutar riki tsakanin gwamna da mataimakin sa.

Abdullahi Ganjuje yace karkashin shugabancin sa, zai duba yuyuwar shirya taro domin tattauna hanyoyin da za’a bi domin kyautata alaka tsakanin gwamnoni da mataimakan su.

Abdullahi Ganduje ya godewa kungiyar tsoffin mataimakn gwamnanonin bisa wannan ziyarar, inda ya tabbatar musu cewa jam’iyyar APC zata kara samun babban cigaba a karkashin mulkin sa.Tunda farko, tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia Chris Akomas, wanda ya jagoranci tawagar, yace sun kai ziyarar ne domin taya Ganduje zama shugaban jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: