Hukumar Kwastam a jihar Ogun ta kwace harsashi guda 1,245 wanda ake zargi ake boye su a buhunan shinkafa yar kasar waje a jejin Tomnolo kusa da karamar hukumar Yewa da ke jihar Ogun.
Kwamandan hukumar a yankin Bamidele Makinde shine ya bayyana haka a Abeokuta babban birnin jihar. Ya kuma kara da cewa ana cigaba da bincike domin gano wadanda ke da alhakin yin fasa kwaurin alburusan.