Ganduje ya nada Jega Shugaban Sabuwar jami’ar Kano.

0 180

Gwamnatin jihar kano ta nada sanata Moshood Olaken Ishola Balogun Aliiwo da farfesa Attahiru Jega a matsayin shugaban jami’a da shugaban kwamatin gudanarwa na sabuwar jami’ar jihar Sa’adatu Rimi Kumbotso.
Sanarwar hakan na kunshen cikin wata wasika da kwamashinan harkokin cikin gida da yada labarai na jihar Mallam Muhammad Garba bayan taron majalisaar zartarwa.
Wannan ya biyo bayan amincewar da hakumar lura da jami’i’o a matsayin jami’a mallakin jiha ta 61 kuma jami’a ta 222 a jadawalin jami’o’in kasar nan.
Nadin shugabannin jami’ar na tsawon wa’adin shekaru 4 wa’adin farko da wasu shekaru 4n na wa’adi na biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: