Majalisar zartarwa ta Jihar Kano ta amince da kashe naira biliyan kusan tara (N8, 980, 303, 460.63) domin gina gada mai suna Muhammadu Buhari a kan Titin Maiduguri da ke ƙwaryar birnin na Kano.

Majalisar ta amince da kashe kuɗin ne jim kaɗan bayan kammala zamanta na mako-mako a ɗakin taro na Africa House da ke fadar gwamnatin jihar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai Muhammad Garba ya ce wannan yunƙuri na cikin burin gwamnatin Abdullahi Ganduje na gina tituna da hanyoyi domin mayar da Kano “hamshaƙin birni” da kuma haɓaka harkokin kasuwanci.

A cewarsa: “Kasancewarsa birni mai tasowa kuma cibiyar kasuwanci a Najeriya, Kano na samun ƙaruwar ‘yan kasuwa da ke shigowa, abin da ya sa ake buƙatar sake tsarawa da haɓaka tituna don ya iya ɗaukar masu zirga-zirga a cikinsa.”

A makon da ya gabata ne tsohon gwamna kuma jagoran adawa a jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki aikin gadar, yana mai cewa “mutanen kano sun fi bukatar ilimi” ba gada ba.

Kazalika, kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kashe naira miliyan 44,300,000 domin yi wa Kwalejin Harkokin Noma ta Audu Bako da ke Ƙaramar Hukumar Dambatta kwaskwarima.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: