Garin Dadi: Shugaban Kasar Amurka Donald Trump Zai Rarraba Kudi Ga Yan Kasar

0 174

Shugaban Kasar Amurka, Donald Trump ya ce tura kudade kai tsaye zuwa ga Amurkawa a matsayin kudaden karfafa tattalin arziki na Dala Biliyan 850 shine ya fi sama da tsarin shigar da kudaden cikin albashi.

Sakataren Baitulmali, Steve Mnuchin ne ya baiyanawa manema labarai sabon tsarin a ganawar da yai da su a ranar Talatar da ta gabata.

Ya ce shirye-shirye sun yi nisa na tura takardun cirar kudade ga Amurkawan.

Adadin kudaden da za’a turawa Amurkawan bai tabbata ba, amma an jiyo wasu ‘yan siyasar da suka hada da dan jam’iyyar Republican, Senator Mitt Romney na cewa za’a tura Dala 1,000.

Sakataren Baitulmalin, Steve Mnuchin, ya tabbatar da cewa wannan na daya daga tsare-tsaren da ake da su, amma bai hada da manyan masu kudiba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: