Garuruwa 94 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa na kwanaki 5

0 153

Gwamnatin tarayya ta yi hasashen cewa garuruwa 94 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa na kwanaki biyar daga jiya Talata 16 ga watan Yuli zuwa ranar asabat 20 ga Yuli, 2024.

Karamin Ministan Muhalli, Dokta Iziaq Salako ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Talata.

Salako ya ce, wuraren da aka gano da muhallinsu za su ga an samu ruwan sama kamar da bakin kwarya wanda zai iya haifar da ambaliya cikin lokacin hasashen.

Ya lissafa jihohin da abin ya shafa da suka hada da  jihar Adamawa; Abiya; Anambra; Akwa Ibom; Bauchi; Bayelsa; Borno; Cross River; Nasarawa; da Babban Birnin Tarayya Abuja.

Sauran su ne Jigawa; Kano; Kebbi; Katsina; Kwara; Nijar; Filato; Koguna; Sokoto; Taraba; Yobe; da kuma jihohin Zamfara. 

Sai dai Salako ya bukaci masu ruwa da tsaki a kasar da su shawo kan matsalar ambaliyar ruwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: