Gwamatin jihar Kano ta rage kudin makarantun gaba da sakandire ga dalibai yan asalin jihar

0 237

Kwamishinan ilimi mai zurfi, Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce an dauki matakin ne don ganin an rage wa al’ummar jihar matsalar kudi ta yadda za a rage kudin rajistar daliban ‘yan asalin jihar a fadin makarantun jihar.

Ya ce an yanke wannan shawarar ne a yayin ganawar da shugabannin manyan makarantu da gwamnan jihar da yammacin ranar Talata a babban birnin jihar.

Hakan yasa za’a ragewa iyayan yara tasirin wahalar tsadar rayuwa da ake fama da ita, bayan janye tallafin man fetur, lamarin da ya haddasa tsadar kayan abinci. Don haka duk ’yan asalin Jihar Kano da ke karatun kwasa-kwasai na yau da kullum a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote, Wudil; Yusuf Maitama Sule University, Kano; Sa’adatu Rimi University of Education, Kumbotso; Aminu Kano College of Legal and Islamic Studies, Kano State Polytechnic; Audu Bako College of Agriculture, Dambatta; Rabiu Musa Kwankwaso College of Advanced and Remedial Studies, Tudun Wada; Kwalejin Ilimi da Nazarin Farko ta Jihar Kano, za ta ci gajiyar jimlar rage kashi 50% na kudin rajista a cikin zaman karatu na 2023/2024.

Leave a Reply

%d bloggers like this: