Majalisar dinkin duniya tayi kira ga ECOWAS da suyi janye takunkuman da suka kakabawa jamhuriyar Nijar

0 210

Majalisar dinkin duniya da kungiyoyin bada agaji sunyi kira ga kungiyar kasashen raya tattalin arzikin afrika ta yamma ECOWAS da suyi janye takunkuman da suka kakabawa jamhuriyar Nijar sakamakon juyin mulki da kayi a kasar, lamarin da ya jefa lafiyar yan kasar cikin wani mawuyacin hali.

Jami’in kula da yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya a Nijar Emmanuel Gignac, yace babu hanyoyin isar da kayan agajin zuwa kasar.

Ya bayyana cewa al’amura na kara tsananta a Nijar din, tun bayan da Najeriya ta yanke mata wutar lantarki, a’umma a kasar sun dogora ne kadai da amfani injinan janareto, sannan kuma ana samu kalubalan samun man fetur.

Bayan juyin mulki da sojoji sukayi ranar 26 ga watan daya gaba ta, wasu kasashe masu makotaka da Nijar din sun rufe iyakokin su da kasar a wani mataki na matsawa jagororin juyin mulki namba su maida mulkin farar hula a kasar.

Manyan jami’an majalisar dinkin duniya masu ofis a kasar, sun rubutawa kungiyar ECOWAS wasikar neman ta janye takun-kuman da suka kakabawa Nijar.

Kungiyar bada agaji ta kasa da kasa na daga cikin gwamnan hukumomin da sukayi irin wannan kira, suna masu cewa janye takunkuman yana da matukar mahimmanci domin a samu damar isar da kayan agaji ga mabukata a Nijar din musamman kananan yara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: