Babu wanda ya isa ya kore ni daga PDP – Wike

0 224

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ƙalubalanci jam’iyyarsa ta PDP kan barazanar korarsa, yana mai cewa babu wanda ya isa.

A lokacin wata tattaunawa da ya yi da kafar Talabijin Channels, ministan ya ce, ba ya tsoron kowa kuma abin da ya ke yi babu batun saba ƙa’idar jam’iyya ko kuma zagon-ƙasa.

Wike wanda tsohon gwamnan Ribas ne, ya ce shi dai a iya saninsa bai ga wani shugaba a PDP da ya ke da ikon iya korarsa ba, ko yi masa barazana.

Ministan ya kuma jadadda cewa shi shugaba Tinubu ya ke yiwa aiki, ba wai APC ba don haka babu wanda ya ke bin sa bashi ko ya wajaba ya nemi afuwa daga gareshi.

Sabon ministan na Abuja ya kuma shaida cewa nan da watanni takwas za a ga canji sosai a birni, saboda jirgin ƙasan da zai ke yawo a cikin gari zai soma aiki, sannan mulkinsa zai dawo da abubuwa sosai musamman ainihin tsarin Abuja.

Wike ya ce har yanzu yana nan kan akidar sa ta kasancewa jigo a PDP.

Jigon na jam’iyyar PDP kuma jagoran kungiyar G5 a zaben 2023 sun kauracewa tarukan jam’iyyar na yakin neman zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: