Akalla mutane dubu 23 ne suka bace bat sanadiyyar tada kayar baya da garkuwa da mutane

0 256

Gwamnatin tarayya a jiya ta ce akalla mutane dubu 23 ne suka bace bat a wasu ayyuka da suka hada da tada kayar baya, garkuwa da mutane da har yanzu ba a gansu ba.

Ministar harkokin jin kai da walwala da yaki da fatara, Betta Edu, wacce ta bayyana hakan a wani taron tunawa da ranar bacewar mutane ta kasa da kasa da hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa ta shirya, ta ce har yanzu ba a tantance ainihin adadin mutanen da suka bace a kasar ba.

Edu, wanda ta samu wakilcin Daraktan Agaji Ali Grema a wurin taron, ta ce ana bukatar ingantacciyar hanya don inganta bayar da rahoto da kuma gano mutanen da suka bata. Tun da farko, shugaban tawagar ICRC a Najeriya Yann Bonzon, ya ce ‘yan uwan mutanen da suka bace an bar su da bakin cikin rashin sanin makomarsu ko inda ‘yan uwansu suke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: