

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya kai ziyarar jaje Jihar Zamfara game da hare-haren ‘yan fashin daji na baya-bayan nan a madadin kungiyar gwamnonin arewa maso gabas.
Zulum wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin, ya kai ziyarar ce a jiya a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Yayin ziyarar, gwamnan ya bai wa wadanda tashin hankalin ya shafa tallafin naira miliyan 20.
Ya bayyana lamarin da jawo kisan mutane 58 a kauyuka 8 na kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da lamari mai tayar da hankali.
Da yake yi wa sarakunan gargajiyar yankin da kuma jami’an gwamnatin Zamfara jawabi, Gwamna Zulum ya nemi al’ummar jihar da kar su karaya, yana mai ambato irin barnar da yakin Boko Haram ya haddasa a jiharsa ta Borno.
Da yake karbar cakin kudin, Gwamna Matawalle ya godewa kungiyar bisa hadin kan da suke bashi, tare da alkawarin aiki tare domin kawo karshen halin rashin tsaro a jihar.