Tawagar hadin gwiwa ta ‘yansanda da sojoji sun ceto mutum 32 da aka sace daga gurare daban-daban a jihar Zamfara

0 91

Tawagar hadin gwiwa ta ‘yansanda da sojoji sun ceto mutane 32 da aka sace daga gurare daban-daban a jihar Zamfara.

Da yake yiwa manema labarai jawabi a helkwatar ‘yansanda dake Gusau, kakakin yansanda a jihar Zamfara, Mohammed Shehu, yace mutanen da aka sace sun fito ne daga jihoshin Neja da Katsina da kuma Zamfara.

Mohammed Shehu yace an duba lafiyar mutanen tare da mika su ga iyalansu.

An ceto 10 daga cikin mutanen bayan an sace su akan hanyar Sheme zuwa Funtua a ranar Alhamis.

Kazalika, kasa da awanni 24 bayan kashe mutane 11 a kauyen Kurmin Masara daga masarautar Atyap a karamar hukumar Zangon Kataf dake jihar Kaduna, ‘yan bindiga sun kaddamar da wani harin a Atisa dake Kurmin Masara.

Wata majiya daga kauyen dake makotaka ta tabbatar da harin ga manema labarai.

Shugaban matasan masarautar Atyap, Gabriel Joseph, shima ya tabbatar da lamarin, inda ya kara da cewa maharan na da shirin kashe su gabadaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: