

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
‘Yansanda sun kama wani ma’aikacin lafiya a jihar Sokoto mai suna Abubakar Hashimu, bisa laifin hada kai da ‘yan fashin daji a jihar Sokoto.
A lokacin da ‘yansanda ke gabatar da shi a jiya da yamma, Abubakar Hashim yace wani mutum ne mai suna Musa Kamarawa ya hada shi da ‘yan fashin daji.
A bara ‘yansanda suka kama Musa Kamarawa.
Musa Kamarawa ne ya ambaci sunan Abubakar Hashim da sauran masu hada kai da ‘yan fashin daji, lokacin da ‘yansanda ke yi masa tambayoyi.
Yace yana shagonsa na sayar da magani lokacin da Musa Kamarawa ya gayyace shi zuwa daji domin duba lafiyar Bello Turji da sauran ‘yan bindigar da sojoji suka jikkata.
Kazalika ‘yansanda sun gabatar da wani mutum mai suna Samuel Chinedu da yake kai wa ‘yan fashin daji magani.