Gwamnan Filato Caleb Muftwang ya karyata jita-jitar cewa zai fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC
Gwamnan Jihar Filato, Caleb Muftwang, ya karyata jita-jitar cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC.
A wata hira da ya yi da BBC, Muftwang ya bayyana cewa maganar ba ta da tushe kuma wani yunkuri ne na jawo hankalin jagororin PDP su sauya sheka.
Ya ce an warware dukkan sabani da ke cikin jam’iyyar a jihar, bayan shawarwarin sasanci da aka yi.
Gwamnan ya ce yana da yakinin jam’iyyar za ta ci gaba da samun goyon bayan jama’a a Jihar Filato da ma ƙasa baki ɗaya.