Gwamnan jihar Benue ya fara yunkurin karin albashi mafi karanci ga ma’aikatan jihar

0 205

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Tersoo Kula ya fitar a yau Juma’a, ta ce tuni gwamnan ya kafa kwamitin da zai duba mafi karancin albashin a halin yanzu tare da bayar da shawarwari ga gwamnati.

Ya ce kwamitin da sakataren gwamnatin jihar ke jagoranta tare da shugaban ma’aikata da kuma shugabannin sassan Hukumomi da dama za su hada kai da kungiyar kwadago ta Najeriya reshen jihar. A cewar Kula, gwamnatin jihar ta na da masaniya kan matsalar tattalin arziki da ke addabar ‘yan kasa, yana mai jaddada cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa don rage radadin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: