An ceto fasinjoji 14 da wasu ‘yan bindiga suka sace a jihar Katsina

0 130

Tawagar jami’an tsaro ta hadin gwiwa da ta kunshi ‘yan sanda, sojojin Najeriya, da kuma ‘rundunar wanzar da zaman lafiya ta jihar Katsina sun ceto fasinjoji 14 da wasu ‘yan bindiga suka sace a jiya Alhamis.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana haka a daren jiya a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 1:30 na rana inda wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka tare wata motar bas ta jihar Katsina) da ke tafiya tsakanin Funtuwa zuwa Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar dauke da bindigogi kirar AK-47 sun tare motar bas din ne a kauyen Gidan Kifi dake kan titin Marabar zuwa Kankara inda suka yi awon gaba da dukkan fasinjojin da ke cikin motar. Sai dai ASP Sadiq ya bayyana cewa, sun samu samun nasarar ceto 14 daga cikin 18 da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: