Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce nasarorin da ya samu a rayuwa da kuma daukakar tafiyarsa ta siyasa nufi ne na Allah.
Gwamna Fubara ya ce Allah ya daukaka shi sanadiyyar shuwagabanni da ‘ya’yan jam’iyyarsa ta PDP, da suka amince su gabatar da shi a matsayin dan takararsu na gwamna domin ya ci zabe.
Fubara ya bayyana haka ne a taron 2024 na Fatakwal a wani Cocin Redeemed lokacin da yake gabatar da jawabi, a yayin taron wanda ya gudana a filin wasa na Adokiye Amiesimaka a jiya Lahadi.
Gwamnan ya bayyana taken taron a matsayin kyauta na kashin kansa domin ya nuna labarinsa.