An samar da kotun tafi da gidanka domin hukunta masu karya dokokin tsaftar muhalli a jihar Jigawa

0 213

Gwamnatin jihar Jigawa ta samar da kotun nan tafi da gidanka domin hukunta masu karya dokokin tsaftar muhalli, wannan dai na zuwa ne yayin da gwamna Mallam Umar Namadi ya jagoranci membobin majalisar zartarwa da sauran mukarraban gwamnatin jiha wajen aikin tsaftar muhalli na karashen wata.

Kwamashinan muhalli na jiha Dr. nura Ibrahim Dandoka ya bayyana haka, lokacin da yake amsa tambayoyin yan jarida a Dutse, a ranar asabat data gabata.

Dr. nura yace an samar da kutunan ne a dukkan masarautun jiha 5 da ake dasu.

A cewar dokar tsaftar muhalli ta jiha, ya zama wajibi a takaita kowace irin zirga-zirga daga karfe 7 na safe har zuwa karfe 10 na safe, ga kowane magidanci domin tsaftace muhallai a duk ranar asabat din karshen wata. A cewar kwamashinan, yayin aikin, ba’a daukewa kowa ba, ana sa ran kowane dan jiha ya bayar da gudunmawa, kuma akwai doka mai Tsauri yayin da kutunan tafi da gidanka zasu rika zagayawa domin tabbatar da cewa ba’a karya dokokin ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: