Gwamnati ta lalata hauren giwa mai ƙimar tsabar kuɗi har dala miliyan 11
Gwamnatin tarayya ta lalata tarin hauren giwa mai ƙimar tsabar kuɗi har dala miliyan 11 da ta ƙwace daga hannun masu fasa-ƙwauri.
An dai yi fasaƙwaurin hauren ne daga ƙasashen Afirka da dama.
Ministan Muhalli na kasa, Iziaq Adekunle Salako wanda ya shaida hakan yayin wani taro a Abuja, ya ce ya ɗauki matakin lalata tarun hauren giwar ne domin aike saƙon da ke nuna rashin amincewarsu ga irin wannan aiki.
Masana sun ce ana kashe dubban ɗaruruwan giwaye a kowace shekara domin yin safarar haurensu, duk da haramcin cinikayyarsu da duniya ta yi shekaru da suka gabata. Masu kare dabbobi sun ce Najeriya ta zamo a gaba-gaba wajen safarar sassan dabbobi.