Hukumar Kidaya ta koka kan karancin hadin kai da take samu daga al’ummar jihar Osun

0 131

Hukumar Kidaya ta kasa ta koka akan karancin hadin kai da take samu daga al’ummar jihar Osun a lokacin rangadin da take gudanarwa na tattara alkaluma na shekarar 2023/2024.

Tawagar wadda Olusola Kari, yake jagoranta, a lokacin da yake yiwa manema labarai jawabi a Osogbo a jiya Talata, yace kundin bayanan da zasu karba daga shirin shine zai bayarda dama ga gwamnati ta samarda tsare-tsare masu kyau, musamman ma akan lamuran da suka shafi fannin lafiya.

A lokacin da yake bayyana irin kalubalen da ma’aikatan su suka fuskanta yain aikin, ya bayyan cewa jami’an Hukumar Kidayar sun ziyarci kananan hukumomin Ede ta arewa, da Ede ta kudu, Ifelodun da Boripe dake jihar, amma al’umman yankunan basu bayar da hadin kai ba. Ya bukaci shuwagabannin kananan hukumomin da su wayarda kan al’ummar yankunan su domin samun nasarar shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: