Gwamnatin jihar Bauchi ta bukaci goyon baya da tallafin asusun TETFund

0 140

Gwamnatin jihar Bauchi ta bukaci goyon baya da tallafin asusun tallafawa manyan makarantu na TETFund ga jami’oi mallakar jihar domin bunkasa fannonin horar da aikin noma da sauran fannonin da zasu kawo cigaban kasar nan.

Gwamna jihar Bala Mohammed, shine ya bayyana hakan a jiya, a lokacin da ya ziyarci ofishin na TETfund a Abuja, inda yace akwai bukatar samarda inganta rayuwar al’umma domin samun nasara wajen yaki da yunwa da kuma rashin ayukkan yi.

A cikin wata sanarwa da Asusun ya fitar a yau laraba, ya Ambato Bala Mohammed na cewa jihar na bukatar tallafi a sabuwar kwalejin ilimi ta jihar da kuma cibiyar koyarda dalibai ayyukkanyi da suka hadar da aikin Gini, Walda da dai sauran su.

Gwamna Bala Mohammed yace kwalejin ilimin zata horas da jami’an aikin Gona da su koyarda al’ummar jihar yadda zasuyi Noma, inda yace gwamnatin sa ta samar da ababen more rayuwa a jami’ar jihar da kudin su yakai kimanin naira Biliyan 3 domin tabbatar da cewa jami’ar ta samu ingantattun tituna, ruwan sha, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: