Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kimanin Naira biliyan hudu da rabi a duk shekara kan dalibai

0 139

Gwamnatin jihar Jigawa zata kashe kimanin naira biliyan hudu da rabi a duk shekara wajen biyan kudaden yan makaranta.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan a jiya a wajen taron bayarda tallafin karatu ga dalibbai 150 da zasu karanci fannin shari’a karkashin shirin tallafin karatu na gwamnatin jiha.

Ya bayyana cewa wannan na zuwa ne bayan kara kudin alawus ga dalibai yan makaranta da kashi 100 domin baiwa dalibai yan asalin jihar nan damar ci gaba da karatun su a matakai daban-daban.

Gwaman ya kuma ce gwamnatin jiha ta bayarda umurnin fitar da kudin da suka kai kimanin naira miliyan 24 domin biyan kudin makarantar dalibai 24 da suke karatun fannin shari’a Akan haka ya jajjadda kudurin gwamnatin sa na ci gaba da zakulo dalibai yan asalin jiha masu karamin karfi domin tallafa musu da kudade domin ci gaba da karatun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: