Gwamnatin Bola Tinubu ta kuduri aniyar inganta fannin kiwon lafiya a Najeriya

0 211

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jaddada kudirin wannan gwamnatin a kokarin da take na samar da kiwon lafiya a cikin gida,da kuma inganta wuraran neman lafiya domin inganta fannin kiwon lafiya a kasar nan.

Kashim Shettima ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakuncin tawagar jami’an kiwon lafiya na duniya, da asusun kiwon lafiya na duniya, da kuma wasu jami’an yaki da cuta mai karya garkuwar jiki daga kasar Amurka,a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Cikin wata sanarwa da daraktan  yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa Olusola Abiola ya fitar, yace shattima ya jaddada kokarin gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na inganta fannin lafiya a Najeriya.

Ya kara da cewa shugaban kasa yana da manufa mai kyau wajen ganin kiwon lafiya a Najeriya ya samu cigaba yadda ake bukata.

Mataimakin shugaban kasar ya bukaci asusun lafiya na duniya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya da bada goyan bayan su ga gwamnatin Najeriya domin cimma manufar shugaban kasar ga Yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: