Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta musanta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da Rasha

0 120

Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta musanta rahotannin da ke cewa ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta soji da kasar Rasha.
Ma’aikatar sadarwa da yada labarai ta kasar ta bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis cewa, babu wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta soji da aka rattabawa hannu kwanan nan tsakanin Rasha da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Wadannan kalaman na zuwa ne biyo bayan labarin da kamfanin dillancin labaran kasar Rasha TASS ya wallafa a ranar Talata, wanda ke cewa gwamnatin Rasha ta amince da daftarin yarjejeniyar hadin gwiwa ta soja da kasar Kongo.
Kasar Congo ta ce daftarin yarjejeniyar da ake magana a kai, kasashen biyu ne suka kaddamar shi a shekarar 1999, amma har yanzu ba a rattaba hannu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: