Shugaba Tinubu ya aike da sojoji domin ceto dalibai sama da 250 na makarantar Kuriga

0 124

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a jiya Juma’a ya aike da sojoji domin ceto dalibai sama da 250 da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba dasu a makarantar Kuriga da ke jihar Kaduna.

Rahotanni na bayyana cewa harin na jihar Kaduna dai shi ne karo na biyu da aka yi garkuwa da jama’a a cikin mako guda a kasar nan da ta fi kowacce kasa yawan jama’a a nahiyar Afirka, inda wasu gungun ‘yan fashi da makami a kan babura ke kai wa wadanda lamarin ya shafa hari a kauyuka da makarantu da kuma kan manyan tituna domin farautar kudin fansa.

Ma’aikatan kananan hukumomin jihar Kaduna sun tabbatar da harin da aka kai na garkuwa da mutane a makarantar Kuriga a ranar Alhamis, inda suka ce yara 287 ne harin ya shafa.

An harbe akalla mutum guda a yayin harin, kamar yadda mazauna yankin suka tabbatar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: