Dole a gudanar da cikakken bincike kan yawaitar sace-sacen da ake yi a Najeriya – Amnesty

0 102

Ƙungiyar Amnesty International ta ce sace fiye da ƴan gudun hijira a jihar Borno da ɗalibai ɗari biyu da tamanin da bakwai da malamai a yankin Kuriga a jihar Kaduna na nuna gazawar hukumomin gwamnati na kare al’umma daga hare-haren ƴan bindiga da suka kashe dubban al’ummu cikin shekara biyar da ta gabata.

Ƙungiyar, cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Juma’a ta hannun shugabanta a Najeriya, Isa Sanusi, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da mutanen da aka sace domin haɗa su da iyalansu.

A cewar ƙungiyar, dole ne hukumomi su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa kan yawaitar sace-sacen da ake yi a sassa da dama na kasa tare da gabatar da sakamakon binciken ga al’umma sannan su tabbatar an hukunta waɗanda aka samu da hannu a garkuwa da mutane.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa yawan gazawar hukumomi wajen kare mutane abu ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba kuma dole ne a kawo ƙarshen sa.

Amnesty ta kuma yi kira da a tabbatar da waɗanda ke da nauyin samar da tsaro a yankunan da aka yi sace-sacen jama’a su yi bayani kan gazawar da ta jefa rayuwar ɗaruruwan mutane cikin haɗari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: