Gwamnatin Jigawa zata ciyar da mutane 171,900 a kowace rana cikin watan Ramadana

0 247

Gwamnatin jihar jigawa tace zata ciyar da akalla mutane dubu 171 da 900 a kowace rana cikin watan ramadana mai kamawa.

Gwamna Mallam Umar Namadi ya bayyana haka yayin kaddamar da rabon kayayyakin abinci na rage radadi a Dutse, yace gwamnatin jiha tana sa ran ciyar da mutane miliyan 5 da dubu 157 kafin karshen watan.

Yace gwamnatin ta kirkiri gurare 2 a kowace mazaba domin shirin ciyarwar, ya kara da cewa a kowanne wuri ana sa ran ciyar da mutane 300 a kullum buda baki, jumilla mutane dubu 171 da 900 a kowace rana a guraren ciyarwa 573 dake fadin jiha.

Gwamnan yace an samar da shirin ne domin tallafawa mabukata da masu karamin karfi yayin lokacin ibadar azumin. Gwamnan ya kuma yi alkawarin bayar da wani tallafin wanda shugaban kasa Bola Tinubu yayi alkawarin bayarwa ga al’ummar jihar Jigawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: