Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya bayyana addu’a a matsayin babban makamin magance matsalolin wahalhalun da jama’a ke fuskanta a fadin kasa.
Yayi wannan jawabi ne yayi kaddamar da rabon kayan abinci ga a’umma wanda aka gudanar a filin taro na Aminu Kano Triangle dake Dutse.
Gwamnan ya bayyana muhimmancin komawa ga Allah domin samun mafita kan halin daka shiga na matsin tattalin arziki.
Yace gwamnatin jiha data tarayya suna daukar matakai da dama domin shawo kan matsalolin tattalin arziki dana zamantakewa dake damun al’umma.
Kwamishinan ayyuka na musamman Auwalu Sankara yace kayayyakin tallafin da aka raba sun hada da buhun shinkafa dubu 150, dana masara dubu 150 da kuma kwalin taliya dubu 100.
Yace kimanin mutane dubu 648 nezasui ci gajiyar tallafin wanda aka gudanar da nufin rage radadin hauhawar farashin kayayyaki da kuma wahalhalu sakamakon cire tallafin man fetur.