Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin jihohi 14 da makarantun su ke cikin hadari

0 107

Gwamnatin tarayya ta fitar da jerin jihohi 14 da makarantun su ke cikin hadari, dai-dai lokacin da ‘yan bindiga ke ci gaba da kutsawa makarantu suna garkuwa da dalibai.

Shugabar hukumar kula da makarantu Hajiya Halima Iliya ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai, tana mai cewa jihohin sun hadar da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, birnin tarayya Abuja, Kebbi, Sokoto, Plateau, Zamfara da karin wasu guda 3.

Bayanin hukumar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da yara kusan 287 a jihar Kaduna, cikin su guda 28 sun tsere.

Kwana guda bayan nan kuma ‘yan bindigar suka sace daliban tsangaya 15 a jihar Sokoto.

Akalla sama da dalubai, malamai da mata 465 ne aka yi garkuwa dasu cikin makon daya gabata, kuma har yanzu suna tsare a hannun yan bindiga.

An sace daliban wata makarantar Tsangaya 15 a jihar Sokoto a safiyar ranar asabat, kasa da sa’o’I 72 bayan sace dalibai da malamai 287 a jihar kaduna. Kafin nan akalla mutane 200 ne yan bindiga suka sace a sansanin yan gudun hijira dake jihar Borno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: