Gwamnatin jihar Jigawa da hadin gwiwar ta kasar Maroko na aiki domin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana

0 65

Gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar Maroko da jihar Jigawa na aiki domin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da zata inganta makamashin hasken rana domin habaka wutar lantarki a shiyyar Arewa maso Yamma da sauran sassan kasar nan.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da kwamishinan filaye, datsare-tsaren birane na jihar Jigawa, Sagir Musa Ahmed ya yi.

Sagir, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai na kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ reshen jihar Jigawa a Dutse, ya ce za a kaddamar da shirin ne a karamar hukumar Gwiwa da kimanin kadada dubu 200.

Ana sa ran aikin zai taimaka wajen ci gaban samar da wutar lantarki a jihohin da aka ambata da ma kasa baki daya.

Ya bayyana cewa gwamnati mai ci ta jajirce wajen ganin an cimma manufofin da ake kudurta saboda muhimmancinsa ga jihar Jigawa da sauran Jihohin arewa maso yammacin kasar nan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: