Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata

0 374

Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata domin tunawa da cika shekaru 32 da kirkirar jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Hussaini Ali Kila.

A cewar sanarwar, Gwamna Malam Umar Namadi ya taya ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar murnar zagayowar wannan rana.

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi wa Jiha da kasa baki daya addu’a yayin bukukuwan wannan rana.

Ya shawarci ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar Jihar da su yi amfani da hutun kwana guda wajen gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa yanayi mai kyau, zaman lafiya da kuma yin addu’a don aiwatar da manufofin gwamnati da shirye-shiryenta da kuma ayyukan gwamnati. Idan dai za a iya tunawa an kirkiri jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a ranar Talata 27 ga watan Agusta 1991 a lokacin shugaban kasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Leave a Reply

%d bloggers like this: