Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta ci gaba da samar da ruwan sha mai tsafta ga al’ummar jihar, inda kwamishinan ruwa na jihar, Alhaji Ibrahim Garba Hannin giwa, ya bayyana hakan yayin buɗe kwantiragin gina tsarin samar da ruwa da ke amfani da hasken rana a ƙananan garuruwa goma sha tara.
A yayin taron wanda mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin ruwa, Alhaji Ibrahim Adamu Gire, ya wakilta, an ce wannan mataki na daga cikin cika alkawuran gwamnatin jihar na sauƙaƙa rayuwar jama’a ta fuskar ruwa.
Daraktan hukumar samar da ruwa da tsaftar muhalli na ƙananan garuruwa, Injiniya Adamu Garba Kiyawa, ya bayyana cewa za a gina sabbin hanyoyin samar da ruwa da za su dogara da hasken rana domin inganta samun ruwan sha mai tsafta. Ya jinjina wa Gwamna Malam Umar Namadi bisa goyon bayan da yake baiwa ma’aikatar ruwa, yayin da wakilin hukumar kula da tsare-tsare, Injiniya Abbas Alhassan, ya shawarci ‘yan kwangila da su yi aiki mai nagarta, yayin da kamfanoni huɗu suka nuna sha’awar samun aikin.