Gwamnatin jihar Jigawa zata samarda irin kifi domin zubawa a madatsun ruwa

0 113

Gwamnatin jihar Jigawa zata samarda irin kifi daban-daban domin zubawa a wasu madatsun ruwa na mazabar dattawa uku  dake fadin jihar nan

Daraktar kula da sashin kifi ta maaikatar  gona da albarkatun kasa ta jiha, Hajiya Rabi Abdullahi ta bayyana haka alokacin da take kaddamar da zuba irin kifi na karfasa da Tarwada guda dubu goma sha takwas a madatsar ruwa ta Birnin Kudu.

Tace hakan nada cikin kudirin Gwamnati na tallafawa masu kanana sana’o’i wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Hajiya Rabi Abdullahi takara da cewa gwamnati ta kudiri aniyar samar da irin  ne a wuraren da basu da wadataccen kifi sakamakon matsalar janyewar ruwa a yankunan, inda tabada tabbacin mika koken masuntan yankin ga gwamnati.

Shima a jawabinsa,  Daraktan tsare-tsare na maaikatar Alhaji Sani Muazu yace gwamnati ta samarda kifin ne kyauta ga masuntan yankin domin tallafa musu wajen bunkasa tattalin arzikinsu.

Sarkin ruwan Birnin Kudu Malam Sule Nasalla Abebe, ya ya roki gwamnati data taimaka musu wajen gina shingen waya a wasu hanyoyin da kifayen ke zirarewa zuwa makwabtan jihohi. Wasu daga cikin al’ummomin sun bayyana farin cikinsu, tare da bada tabbacin bin ka’idojin da ya kamata wajen yin su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: