Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware Naira biliyan 6 domin daukaka darajar manyan asibitocin da suke Jihar

0 90

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ware Naira Biliyan 6 domin daukaka Darajar Manyan Asibitoci da suke Jihar tare da sayan kayayyakin da suke bukata na Jihar a shekarar 2022.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya bada rahotan cewa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya sanya hannu kan kasafin kudin Jihar na Naira Biliyan 278 da Miliyan 600 na shekarar 2022.

Daftarin ya nuna cewa an ware wa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Naira Biliyan 15 da Miliyan 700 domin gudanar da manyan ayyuka, inda daga cikin kudade kuma aka ware Naira Biliyan 7 da Miliyan 400 domin sake fadada aikin Asibitin Kwararru mai gadaje 300.

Haka kuma Daftarin ya nuna cewa kimanin Naira Miliyan 282 da dubu 900 ne aka ware domin gina sashen killacewa da tare da kulawa da masu cutar Corona da sauran kayan Agajin gaggawa.

Manema Labarai sun rawaito cewa Naira Miliyan 51 da Dubu 600 ne aka ware domin gina tare da daga Darajar Sashen kula da masu bukatar taimakon gaggawa a manyan Asibitocin Kafanchan, Saminaka,Birnin Gwari da kumam Asibitin Hajiya Gambo Sawaba da ke Zaria.

Leave a Reply

%d bloggers like this: